Kotu ta ɗaure tsohon manajan banki shekara 121 kan zambar kuɗi

An samu Nwachukwu Placidus wanda tsohon manaja ne a bankin FCMB da laifin almundahana ta naira miliyan 112,100,000.

Kotu ta ɗaure tsohon manajan banki shekara 121 kan zambar kuɗi

Kotu

Wata kotu a Anambra ta yanke wa tsohon manajan bankin FCMB, Nwachukwu Placidus, hukuncin ɗaurin shekara 121 saboda samunsa da laifin zambar kuɗaɗe.

Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Nijeriya Zagon-Ƙasa wato EFCC ce ta shigar da shi ƙara inda ta zarge shi da almundahana ta naira miliyan 112.

Mai Shari’a S.N. Odili ne ya yanke wannan hukuncin bayan ya samu Nwachukwu Placidus wanda tsohon manaja ne a bankin FCMB da laifin almundahana ta naira miliyan 112,100,000.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an gurfanar da shi ne a ranar Talata 27 ga watan Maris ɗin 2018 kan zarge-zarge 16 waɗanda suka haɗa da laifin yin jabu da sata da ƙarya.

Cikin wata sanarwar da Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce an gurfanar da mista Placidus a gaban kotun ne ranar 27 ga watan Maris ɗin 2018.

An tuhume shi da laifuka 16 da suka haɗa da sata da yin ƙarya a furucinsa da kuma a takardu.

Sanarwar ta ce a lokacin da Placidus ke aiki a matsayin manajan bankin FCMB reshen birnin Onitsha, ya karɓi kuɗi daga wani kwastoman bankin da nufin sanya masa kudin asusun ajiyarsa, amma sai mista Placidus ya karkatar da su.

Bayan gudanar da bincike ne, EFCC ta gano cewa Placidus ya karkatar da kuɗin domin amfanin kansa, inda kuma ya gabatar da takarda ta ƙarya da ke nuna shaidar saka kuɗin a asusun kwastoman, kan hakan ne kuma kotun ta ɗaure a gidan gyaran hali.

Sai dai Mista Placidus ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa bayan an karanto masa su a kotu.

“A lokacin shari’ar, EFCC ta hanyar lauyanta Mainforce Adaka Ekwu ya gabatar da shaidu huɗu waɗanda suka bayar da takardu masu muhimmanci a matsayin hujjoji,” in ji sanarwar.

Mai shari’a Odili ya yanke wa Mista Placidus hukuncin ɗauri na shekara tara bisa zargi na biyu sai hukuncin ɗaurin shekara huɗu kan zargi na huɗu.

Sannan Mai Shari’ar ya yanke masa hukuncin ɗauri na shekara tara-tara kan zargi na biyar har zuwa na zargi na 16.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume