Kotu Ta Ɗaure Wanda Ya Cinye Dukiyar Marayu A Maiduguri
Wata Babbar Kotu a Maiduguri a Jihar Borno ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Umaru Fadawu ta ɗaure wani da aka akama da laifin cinye dukiyar wasu marayu. A ranar Laraba, 24 ga Afrilu, 2024, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta samu nasara a kan Isiyaku Ibrahim, inda aka yanke masa hukunci […]
Wata Babbar Kotu a Maiduguri a Jihar Borno ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Umaru Fadawu ta ɗaure wani da aka akama da laifin cinye dukiyar wasu marayu.
A ranar Laraba, 24 ga Afrilu, 2024, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta samu nasara a kan Isiyaku Ibrahim, inda aka yanke masa hukunci zaman gidan yari har na watanni 12 bisa laifin cinye dukiyar marayu ta Naira miliyan 12..
Sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale ya fitar ranar Litinin ta ce hukumar ta gurfanar da Isiyaku Ibrahim a gaban kotu a ranar 3 ga Yuli, 2023, kan zargin salwantar da karorin marayu.
Da farko dai alƙali ya tambayi wanda aka ɗaure kan abin da ake tuhumar sa, sai ya musanta, dalilin da ya sa aka shiga bincike.
- Mai shago ya sace yarinya ya boye ta a firinji a Kaduna
- Dole a kara kuɗin lantarki ko a rasa ta baki daya —Minista
Bayan zurfafa bincike ne dai alƙali ya tabbatar da cewa Isiyaku ya aikata abin da ake zargin sa da shi na cinye gaon marayun da aka ba shi domin ya kula da ita.
Alƙali ya ce, “laifin na Isiyaka ya saɓa wa kundin dokar final kod da dokar zamantakewa ta Jihar Borno.
“Dan haka an yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata shida ko kuma tarar Naira dubu ɗari.”