Kotu ta aike da Jaruma mai ‘Kayan Mata’ gidan gyaran hali
Kotun dai ta aike da Jaruma zuwa gidan gyaran hali na garin Suleja.
Wata kotun majistare da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ta aike da ’yar kasuwar nan da ke sayar da kayan mata, Hauwa Muhammad, wacce aka fi sani da Jaruma, zuwa gidan gyaran hali.
Tun da farko dai ’yan sanda masu shigar da kara sun zargeta ne da yada labaran karya, barazana da kuma bata suna.
- Zulum ya ziyarci iyayen wanda Boko Haram suka sace a Chibok
- Masarautar Bauchi ta tube rawanin Yakubu Dogara
Alkalin kotun, Mai Shari’a, Ismaila Abdullahi l, ya sanya ranar Juma’a don yanke hukunci.
Ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun 2022, inda ya ba da umarnin a garkameta a gidan gyaran hali na garin Suleja a Jihar Neja, har zuwa lokacin.
Tun da farko dai, lauyoyi masu shigar da kara, E. A Inegbenoise da Chinedu Ogada, sun shaida wa kotun cewa wanda yake korafin, Ned Nwoko, ya kai karar Jaruma ta hanyar wani korafi da ta aike a rubuce ga ofishin ’yan sanda na Abuja ranar 20 ga watan Janairu don yin bincike a kai.
Mista Inegbenoise ya ce Jaruma ta yi amfani da kafafen sada zumunta da dama, musamman shafinta na Instagram wajen wallafa bayanan karya a Ned Nwoko da matarsa, Regina.
Ya kuma yi ikirarin cewa Jaruma ta yi amfani da shafin nata na Instagram wajen cewa ta ba Regina Daniels din kwangilar Naira miliyan 10 don ta tallata mata kayan matan.
Lauyan ya kuma ce wacce ake karar ta yi zargin cewa mai kara da matarsa sun karbi kudin nata amma suka ki tallata mata haja, a kwangilar da ba a taba ma kullata ba.
Ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 392, 393, 397 da na 418 na kundin final kod.
Sai dai wacce ake karar ta musanta laifukan da ake zarginta da su.