Kotu ta aike da Murja zuwa gidan yari
Kotun Musulunci ta aike da matashiyar nan da ke ashe a TikTok, Murja Ibrahim Kunya, zuwa gidan yari.
Kotun Musulunci ta aike da matashiyar nan da ke ashe a TikTok, Murja Ibrahim Kunya, zuwa gidan yari.
Kotun da ke zamanta a Filin Hoki a birnin Kano ta ba da umarnin tsare Murja a gidan yari ne bayan matashiyar ta musanta tuhume-tuhumen da ake mata.
A zaman kotun da ke karkashin Mai Shari’a Shari’a Abdullahi Halliru a ranar Alhamis, an tuhumi Murja Kunya da bata suna da kuma barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.
Bayan Murja ta musanta tuhume-tuhemen da Barrista Lamido Abba Soron Ɗinki ya karanto ne kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Bayan dage sauraron karar, lauyan Murja, Barista Yasir Musa, ya nemi kotun ta tura ta zuwa ofishin hukumar Hisbah maimakon gidan yari, amma kotun ta yi watsi da bukatarsa.