Kotu ta aike da ’yan Yahoo 4 gidan yari

Kotun ta yanke musu da hukuncin zaman gidan kaso ko kuma biyan tara.

Kotu ta aike da ’yan Yahoo 4 gidan yari

Wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifi (Daga taskarmu).

Mai Shari’a Efe Ikponmwonba na Babbar Kotun Jihar Edo, ta yanke wa wasu ’yan damfarar intanet hudu hukuncin dauri a gidan yari, bisa samun su da laifin zamba cikin aminci.

Jami’an Hukumar EFCC ne suka gurfanar da ’yan Yahoo din a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume masu alaka da zamba cikin aminci, yaudara da kuma damfara.

Bayan gurfanar da su gaban kotu, wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu.

Sai dai lauyan masu shigar da kara, K.U. Udus da I.K. Agwa ya roki kotu da ta yanke musu hukuncin da ya dace.

Mai shari’a Ikponmwonba ta yanke wa uku daga cikinsu hukuncin daurin shekara uku a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira 200,000.

Na hudu kuma aka yi masa daurin shekara biyu a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira 200,000.

Kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 10 ga watan Janairun 2023.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya