Kotu ta ba Atiku damar ya aike takardar sammaci ga Buhari

A shekaranjiya Laraba ce Kotun Daukaka Kara da ke sauraron kararrakin zabe, ta ba Jam’iyyar PDP da dan takararta Alhaji Atiku Abubakar damar su aike da takardar sammaci ga Shugaba Muhammadu Buhari bisa tuhumar da suke yi masa da Jam’iyyar APC cewa ba su lashe zaben Shugaban Kasa da aka yi a ranar 23 ga […]

Kotu ta ba Atiku damar ya aike takardar sammaci ga Buhari

A shekaranjiya Laraba ce Kotun Daukaka Kara da ke sauraron kararrakin zabe, ta ba Jam’iyyar PDP da dan takararta Alhaji Atiku Abubakar damar su aike da takardar sammaci ga Shugaba Muhammadu Buhari bisa tuhumar da suke yi masa da Jam’iyyar APC cewa ba su lashe zaben Shugaban Kasa da aka yi a ranar 23 ga Fabrairun bana ta sahihiyar hanya ba.

Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ne suka shigar da karar a gaban kotun inda suka nemi kotun ta ba su damar aike takardar sammaci ga Shugaba Muhammadu Buhari ko da ta jaridu ne ganin yadda suke samun matsala wajen tuntubar Shugaban Kasar kai-tsaye kan wannan batu.

Kotun wadda ke da wakilai uku a karkashin jagorancin Mai shari’a Abdul Aboki, ta kuma ba Jam’iyyar PDP da Alhaji Atiku Abubakar damar aika takardar sammaci ga Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC ne bayan Lauyan mai kara, Chris Uche (SAN) ya gabatar da bukatar haka a zaman kotun na farko a shekaranjiya Laraba a Abuja.

Kotun ta ba Jam’iyyar PDP da Alhaji Atiku Abubakar damar su aika takardar sammacin kai-tsaye ga Shugaba Buhari ko ta hannun na kusa da shi ko ta sakatariyar Jam’iyyar APC ko ta jaridu don sakon ya isa gare shi.

Mai shari’a Aboki ya ce kotun ta yi haka ne “don a yi wa kowane bangare adalci.”

Baya ga Jam’iyyar PDP da ta shigar da kara a gaban kotun da ke sauraren karararraki kan zaben shugaban kasa na 2019 an samu wasu jam’iyyu uku da su ma suka bi sahun jam’iyyar suna kalubalantar nasarar Shugaba  Buhari da Jam’iyyar APC, inda suka ce za su kai kara game da sahihancin sakamakon zaben.

Jam’iyyun da suka hada kai da PDP wajen shigar da kara sun hada da Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) da Coalition For Change (C4C) da kuma People’s Democratic Mobement (PDM).