Kotu ta ba da belin likitan da ke yi wa masu neman haihuwa cikin bogi
Wata Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja, ta ba da belin wani likitan gargajiya da aka kama kan zargin yaudarar mata masu neman haihuwa cewa suna da ciki, inda daga baya sai ya dauki jariran wadansu ya ba su ya karbi kudi daga gare su. An kama mutumin ne bayan ya yi wa wata mace da […]

Wata Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja, ta ba da belin wani likitan gargajiya da aka kama kan zargin yaudarar mata masu neman haihuwa cewa suna da ciki, inda daga baya sai ya dauki jariran wadansu ya ba su ya karbi kudi daga gare su. An kama mutumin ne bayan ya yi wa wata mace da ke neman haihuwa cikin bogi ta hanyar ba ta maganin gargajiya.
Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP) ce ta kama mutumin mai suna Chigozie John Emmanuel da aka fi sani da Akuchi mai shekara 38 wanda ya fito daga Jihar Enugu a karshen watan jiya a asibitinsa mai suna Akuchi Herbal Concept da ke garin New Nyanya a karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, sannan bayan bincike ta gurfanar da shi a kotun inda ya bukaci beli, amma ya gaza cika ka’idojin belin.
Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin a ranar Litinin da ta gabata ya tarar da shi a rufe tare da jan rubutu da ke dauke da sunan Hukumar NAPTIP, kuma da ya ziyarci hedkwatar Hukumar NAPTIP da ke Abuja, kan lamarin, Babban Jami’n Hulda da Jama’a na Hukumar, Mista Josiah Emerol ya shaida masa cewa sun sake neman amincewar kotun na su ci gaba da tsare wanda ake zargin kamar yadda doka ta nuna, kuma suna dakon ranar fara sauraron shari’ar da zaran kotun ta sanya lokaci.
Wani bayani da kotun ta raba wa manema labarai da Aminiya ta samu kwafi ya nuna cewa, kama mutumin ya biyo bayan kama wata mata ce da ’yan sanda suka yi a kan hanyarta ta zuwa Minna daga Abuja dauke da wani jariri dan kasa da mako daya. Bayanin ya ce a yayin binciken, matar ta shaida wa ’yan sanda cewa ta samu jaririn ne daga wajen mutumin bayan ta ziyarci asibitinsa da nufin ya taimaka mata ta samu haihuwa.
Ta ce mutumin ya ba ta wasu magungunan gargajya inda ta dawo tamkar mai ciki sannan ya gargade ta cewa ta guji zuwa asibti da sunan haihuwu ko wata larurar rashin lafiya. Bayan tsawon lokaci sai ya umarce ta da ta je garin Fatakwal inda za ta haihu kuma a can din ne ya danka mata jaririn. Ta ce ta kashe Naira dubu 650 a matsayin kudin dawainiya da ya yi mata a tsawon wannan lokaci.
Kakakin Hukumar NAPTIP ya ce bayan sa ido na tsawon lokaci a asibitn tare da taimakon jami’an tsaro na farin kaya (DSS), hukumar ta samu nasarar kama likitan tare da gudar da bincike a kansa kan zargin laifuffukan da suka hada da sayar da jarirai da kuma safar mutane. Ya ce hukumar tana dakon kotun ta sanya lokacin fara sauraron shari’ar a daya daga cikin rukunin kotunan da ke karkashinta.