Kotu ta ba da belin mutum 20 da ake zargi da hannu a kashe Janar Alkali

Babbar Kotun Jihar Filato ta 5 da ke  Jos a karkashin Mai shari’a Daniel Longji ta ba da belin mutum 20 daga cikin 28 da ake zargi da hannu wajen kashewa da boye gawar Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya). Idan ba a manta ba tun a watan Oktoban da ya gabata ake tsare da […]

Kotu ta ba da belin mutum 20 da ake zargi da hannu a kashe Janar Alkali

Babbar Kotun Jihar Filato ta 5 da ke  Jos a karkashin Mai shari’a Daniel Longji ta ba da belin mutum 20 daga cikin 28 da ake zargi da hannu wajen kashewa da boye gawar Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya).

Idan ba a manta ba tun a watan Oktoban da ya gabata ake tsare da mutum 28 a gidan yari bayan an zarge su da kashewa da kuma boye gawar Janar Alkali wanda aka sanar da bacewarsa tun ranar 3 ga Satumban da ya gabata a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

A lokacin da Mai shari’a Daniel Logji yake bayani kafin ya bayar da belin mutum 20 daga cikin 28 din ya ce, ya saurari dukan bayanan lauyoyin masu kara da wadanda suke kare wadanda ake tuhumar, kafin ya bayar da belin.

Ya ce, “Sashi na 100 da na 138 da na 148 na dokar Final Kod, a karkashin tuhuma ta 3 da ta 4 da kuma ta 5 sun nuna cewa ko da an samu mutum 20 din da laifin da ake zarginsu na boye bayani kan Janar Alkali ko yin taron sirri ba bisa ka’ida ba kan Janar Alkali ko kin amincewa a yi bincike don gano gawar Janar Alkali, to za a iya ba da belinsu.

“Ko da ma wadannan mutum 20 an same su da laifin boye bayani kan Alkali ko yin taron sirri ba bisa ka’ida ba ko kin amincewa a yi bincike don gano Janar Alkali to da yanzu sun kammala zaman wakafinsu.” inji shi.

Ya ce, amma sauran wadanda ake zargin bai samu lokaci wajen bin dukan bayanan lauyoyin masu kara da wadanda suke karewa ba, saboda takardun bayanan karar suna da yawa, “Kuma kafin in yanke hukunci sai na yi nazari da bincike da kuma karanta su sosai,” inji Mai shari’a Longji.

Alkalin ya ba da belin mutum 20 din ne a kan kowanensu zai biya Naira miliyan daya a matsayin kudin beli, sannan kowannensu zai kawo mutum daya da zai tsaya masa, wanda zai rubuta takardar amincewa ga kotu da za ta nuna cewa ya san wanda aka gurfanar a kotun kuma zai kawo shi gaban kotu duk lokacin da ake bukatar haka.

Idan ba a manta ba an gurfanar da wadanda ake zargin ne da laifin kisan kai da hadin baki wajen aikata kisan kai da boye muhimman bayanai kan laifin da aka aikata na kashe Janar Alkali da laifin yin taron sirri ba bisa ka’ida ba kan batun Janar Alkali da kuma hana sojoji su yi bincike don gano gawar marigayi Janar Alkali.

A zaman kotun na ranar Litinin da ta gabata duka mutum 28 din da ake zargi sun kin amincewa da laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

Lauya G.D. Fonyon wanda ya shigar da kara ya ki amincewa a ba da belin wadanda ake zargin, inda ya bayyana wa kotu cewa wadanda ake zargin ana tuhumarsu da laifin aikata kisan kai ne, wanda kuma hukuncinsa shi ne kisa, don haka bai kamata a ba da belinsu ba.

A lokacin da lauyan wadanda ake tuhumar, Jorge Izere yake mayar da martani  ya ce babu laifin da yake da girman da ba za a iya ba da beli a kansa ba.

Ya ce, “Lura da bayanan da muka rubuta muka mika ga kotu muna rokon kotu ta ba da belin wadanda ake tuhumar, domin babu wata doka da ta bayyana cewa ga wani laifi da ake zargin wani ya aikata da ba za a ba da beli a kansa ba.

“Don haka nake bukatar kotu ta ba da belin wadanda ake tuhumar domin hakan ba yana nufin shi ke nan idan an same su da laifi to ba za a hukunta su ba,” inji shi.

Daga nan Mai shari’a Daniel Longji ya ba da belin mutum 20 a cikin 28, sannan ya dage sauraren karar zuwa 25 ga Janairu, 2019.