Kotu ta ba da belin Sanata Misau

A ranar Talatar da ta gabata ne Mai Shari’a Anwuli Chikere na babbar kotun tarayya dake Abuja ya amince ya kuma bada belin Sanata Isah Misau bisa kimar kansa. Haka kuma Alkalin ta umarci dan majalisar da ya jingine fasfon tafiye-tafiyensa zuwa kasashe waje a kotun, amma inda yana bukatar amfani da shi zai rika […]

Kotu ta ba da belin Sanata Misau

A ranar Talatar da ta gabata ne Mai Shari’a Anwuli Chikere na babbar kotun tarayya dake Abuja ya amince ya kuma bada belin Sanata Isah Misau bisa kimar kansa. Haka kuma Alkalin ta umarci dan majalisar da ya jingine fasfon tafiye-tafiyensa zuwa kasashe waje a kotun, amma inda yana bukatar amfani da shi zai rika rubutawa kotun idan  bukatar hakan ta taso. Sannan kuma ta dage sauraron karar har zuwa 21 ga Watan Janairun 2018.

Gwamnatin Najeriya ce dai ta gurfanar Sanata Isah Misau, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, bisa zarge-zargen da ya yi ga Babban Sufeton ‘Yan Sanda na kasa, Ibrahim Idris akan cin hanci da rashawa.

A yayin fara sauraron shari’ar, mai gabatar da kara daga ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Saleh Hadi, ya sanar da kotun sauye-sauyen tuhumar da ake yi wa dan majalisar. Ya ce  “wadannan su ne jerin tuhumar da ake yi wa wanda ake kara kamar yadda kotu ta bada umarnin dage zaman da ya gabata.” Sannan sai ya mika takardun don karantawa wanda ake karar, don bas hi damar kare kansa.

Bayan da aka karanta jerin tuhuma guda 10 ga Sanata Misau, ya musanta dukkan tuhumomin ya kuma nesanta kansa daga gare su. Jim kadan bayan haka, sai lauyan dake kare wanda ake karar, Uchena Ogbunabo, ya nemi kotun ta bada belin wanda yake karewa bisa kimar kansa, wanda kuma kotun ta amsa wannan bukata anan ta ke.