Za a kai Hadi Sirika gidan yari idan… —Kotu

Kotu ta ba umarnin tsare su Hadi Sirika a gidan yari idan ba su cika sharudan beli ba

Za a kai Hadi Sirika gidan yari idan… —Kotu

Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika da ’yarsa Fatimah da wasu biyu a kan Naira miliyan 100 kowannensu. 

Alkalin kotun da ke da ke zamanta a Abuja, Mai Shari’a Sylvanus Oriji, ya ba da umarnin tsare su Hadi Sirika a gidan yari idan ba su cika sharudan belin ba.

Mai Oriji ya shardanta wa kowanne daga cikinsu kawo mutanen kirki biyu da za su tsaya masa, kuma dole kowanne daga cikin mutanen ya kasance ya mallaki gida a Abuja.

Kotun ta kuma haramta wa su Hadi fita kasar waje ba da izinin kotu ba, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranakun 10, 11 da kuma 20 ga watan Yuni, 2024.

Mai Shari’a Shari’a Sylvanus Oriji ya sanar da haka ne bayan an gurfanar da su a safiyar Alhamis kan zargin karkatar da Naira biliyan 4.1 daga asusun gwamnati.

Hukumar Yaki da Masu Karya Arzikin Kasa (EFCC) ce ta gurfanar da Hadi Sirika tare da ’yarsa Fatimah da Jalal Hamma da kuma Kamfanin Al-Duraq Investment Ltd.

Binciken da EFCC ta gudanar ne ya bankado badakalar kwangilar Naira biliyan 4.1 a ma’aikatar sufurin jiragen sama a lokacin jagorancin Hadi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos