Zargin Batanci: Kotu ta ba da umarnin a kamo Dokta Idris Dutsen Tanshi

Kotun ta umarci jami’an tsaro su kamo mata Dokta Idris Abdulaziz bayan ta yi watsi da uzurin rashin lafiya da lauyoyinsa suka gabatar.

Zargin Batanci: Kotu ta ba da umarnin a kamo Dokta Idris Dutsen Tanshi

Dokta Idris Dutsen Tanshi

Kotun Muslunci da ke Bauchi ta umarci jami’an tsaro su kamo mata Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, saboda rashin halartar zamanta na yau Laraba.

Kotun ta ba da umarnin ne a yayin ci gaba da sauraron shari’ar malamin da aka gurfanar gabanta bisa zarign sa da batanci ga Manzon Allah da kuma neman tayar da zaune tsaye, zargin da ya musanta.

Aminiya ta kawo rahoton cewa malamin, wanda kotu ta tsare a gidan gyaran hali, ya koma gida ranar 22 ga watan Mayu bayan da ya cika sharudan belin da kotun ta bayar, bayan zamanta na karshe a kan shari’ar da ta dage zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2023.

Sai dai a yayin ci gaba da zaman kotun, lauyoyin Dokta Idris Dutsen Tanshi sun shaida mata cewa malamin bai samu zuwa ba ne saboda rashin lafiya.

Amma kotun ta yi watsi da uzurin da lauyoyin Dutsen Tanshi suka bayar, ta bayyana hakan a matsayin raina kotu.

Don haka ta umarci jami’an tsaro da su kamo shi domin ci gaba da gurfanar da shi.
Kungiyar Fityanul Islam ce dai ta maka malamin a Kotun Majistare da Jihar Bauchi, bisa zargin sa da kalaman batannci ga  Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.

’Yan sanda suN gurfanar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi bisa zargin tayar da hankulan jama’a.

A kwanakin baya ne wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya, ta rubuta takardar koke ga kwamishinan ’yan sandan jihar, bisa zargin Malamin ya yi batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi).

Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda gayyatar dukkan bangarorin da abin ya shafa inda Dokta Abdulaziz, wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, ya amsa gayyatar ’yan sandan kafin daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan zargi.

Alkalin kotun ya hana bayar da beli, sannan ya bayar da umarnin a ajiye malamin a gidan gyaran hali, tare da bayar da umarin sake dawo da shi gaban kotu ranar Talata.

A watan da ya gabata ma malamin a cikin hudubarsa ta Azumin Ramadana, an zarge shi munana ladabi ga Manzon Allah (SAW).

Sai dai kuma an wasu malaman da suka goyi bayansa da cewa kalamansa na an turba ta gaskiya.

2025: ’Yan Najeriya suke bibiyar abin da shugabanni ke yi – Atiku

Abba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin N719bn na 2025

Mutum 5 da aka fi ambato a 2024 a Afirka

Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai