Kotu ta ba da umarnin sakin Sheikh Sani Zariya
Kotu ta ba da umarnin biyan malamin diyyar jimillar Naira miliyan 5 kan take haƙƙoƙinsa na ɗan Adam.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a saki malamin addinin nan, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya nan take ba tare da wani sharaɗi ba.
A hukuncin da Mai Shari’a Peter O. Lifu ya yanke a ranar Litinin, ta kuma ba da umarnin biyan malamin diyyar jimillar Naira miliyan 5 kan take haƙƙoƙinsa na ɗan Adam.
- Konate zai sabunta kwantaraginsa a Liverpool
- Tinubu ne zai yi nasara a Arewa a Zaɓen 2027 — Iliyasu Kwankwaso
Mai shari’a Lifu ya bayyana cewa tsare malamin na tsawon lokaci ba tare da umarnin kotu ba ya saɓa wa haƙƙoƙinsa na ’yancin kai, sauraron shari’a cikin adalci da kuma ’yancin zirga-zirga kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
A ƙunshin shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/55/2026 da malamin ya shigar kam take masa haƙƙin ɗan Adam, inda malamin ya shigar da ƙara kan hukumomi da EFCC, DIA, Bankin Jaiz da kuma DSS.
Kotun ta umarci Babban Lauyan Tarayya da ya tabbatar da an bi umarnin da kotu ta bayar gaba ɗaya, tare da sakin malamin nan take ba tare da wani sharaɗi ba.
Haka kuma kotun ta bayyana cewa rufe asusun bankin malamin da aka yi ba tare da izinin kotu ba ya saɓa wa doka, inda ta umarci a gaggauta cire takunkumin da aka ƙaƙaba wa asusun nasa.
Mai shari’a ya bai wa EFCC da Bankin Jaiz umarnin biyan malamin diyyar Naira miliyan ɗaya-ɗaya, sakamakon rufe asusunsa ba bisa ƙa’ida ba, yayin da ya umarci DIA da SSS biyan diyyar naira miliyan huɗu saboda take haƙƙin malamin.
Bugu da ƙari, kotun ta umarci DIA da SSS da su rubuta takardar neman afuwar malamin kamar yadda doka ta tanada.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ƙarshen shekarar 2025 aka tsare malamin bayan ya ziyarci Abuja domin warware matsalar kulle asusun bankinsa da ke da alaƙa da wani zargin mu’amalar kuɗi na Naira miliyan 2 da ake bincike a kai.
Tun a zaman kotu na watan Fabrairu da Maris na 2026, gwamnati ta gaza gabatar da sahihan takardun tsare shi, lamarin da ya janyo ƙorafi daga iyalansa kan rashin sanin inda ya shiga.
Kotun ta jaddada cewa dole ne a bi doka wajen tsare duk wani da ake zargi da laifi, tare da kare haƙƙoƙin ’yan ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.