Kotu ta ba da umarnin sayar da kadarorin surukin Buhari
Tun a shekarar 2018 aka ƙulla yarjejeniyar biyan bashin cikin watanni shida.
Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke GRA a Sabon Garin Zariya, ta umarci sayar da kadarorin tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Hon Muhammad Sani Sha’aban domin biyan bashin Dala dubu 709,238 da wasu Naira miliyan 11 da dubu dari biyu da ya karɓa a hannun wani abokinsa, Alhaji Umar Faruq Abdullahi.
Da yake yanke hukunci a ranar Litinin da ta gabata, Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Alhaji Ishaq Madahu, ya kuma ba da umarnin cewa a gaggauta a nemo masu sayen kadarorin Sani Sha’aban domin biyan basussukan.
- Kotu ta aike da Murja gidan gyaran hali kan zargin karuwanci
- Yanzu Muka Fara Kama ’Yan Tiktok —Hisbah
Alƙalin Kotun ya ce matuƙar kuma aka siyar da kadarorin kuɗaɗen ba su kai ba, dole wanda ake kara ya cika ragowar tsabar kuɗin idan kuma kuɗaɗen sun zarce adadin bashi, wajibi ne a mayar wa wanda ake ƙara ragowar kuɗaɗensa.
Kotun ta kuma ce idan hakan bai samu ba shi wanda ake ƙara zai biya bashin ne daidai da kuɗaɗen da ya ranta na Dala da Naira.
Da yake zantawa da manema labarai hukuncin da kotu ta yanke, lauyan masu kara, Kabir Momoh, ya nuna gamsuwarsa dangane da hukuncin, yana mai godiya ga kotun saboda amsa roƙon su dangane da ƙarar da suka shiga.
Sai dai lauyan wanda ake ƙara bai yi magana da manema labarai ba saboda a cewarsa wanda yake karewar bai ba shi damar gabatar da jawabi ga manema labarai ba.
Tun a shekarar 2018 aka karɓi bashin
Tun a watan Disambar shekarar 2022 ne dai aka maka Alhaji Sani Muhammad Sha’aban a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musuluncin da ke Zariya saboda taurin bashi.
Ana dai zargin Sani Sha’aban wanda surukin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne da ƙin biyan bashin kuɗaɗen da da ya ranta shekaru 6 da suka gabata..
Lauya mai kara ya shaida wa kotun cewa a wani lokaci a shekarar 2018, wanda ake karar ya je wajen mai kara a lokacin suna tare da wani abokinsu mai suna Bashir Abubakar, inda shi wadda ake kara ya buƙaci da ya bashi rancen kuɗi har Dalar Amurka miliyan ɗaya da kuma kuɗin Najeriya Naira miliyan 11 da dubu 200.
Kamar yadda lauyan ya ci gaba da shaida wa kotun, ya ce wadda ake ƙara ya bukaci da a samar da bayanan yadda za a biya bashin da kuma yarjejeniya kamar yadda shari’ar musulunci ta tanada.
A cewar lauyan, Alhaji Farouq ya amince da buƙatar Sani Sha’aban wanda kuma ya buƙaci lauyansa, Ismaila Musa Jamoh da ya tsara takardar yarjejeniyar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, takardar yarjejeniyar ta ƙunshin takardun mallakar kadarorin Alhaji Sha’aban domin a amince a ba shi rancen.
Lauyan ya bayyana wa kotun cewa daga cikin kadarorin akwai gini da ke lamba 48 a layin Yusuf daura da Layin Hadeja da ke Bompai a jihar Kano mai lambar mallaka 009234, ai kuma Kamfanin Mazari Ltd wadda ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna a Zariya mai shaidar mallaka KD 6246 a Zariyan Jihar Kaduna.
Sauran kaddarorin sun haɗa da TULIPS da ke mahadar MTD daura da titin Queen Elizabeth GRA Zariya.
Haka kuma, akwai fili da gini a titin Circular GRA Zariya mai lambar mallaka KD 11226 da kuma wani gini da ke bayan gidansa kusa da makarantar Therbow mai lamba 3964.
Lauyan ya kuma shaida wa kotu cewa a lokacin da aka bayar da bashin, Sani Sha’aban yana Dubai, lamarin da ya sa bai sanya hannu a kan takardar da kansa ba, sai lauyansa Ismail Musa Jamoh.
Sai dai Sani Sha’aban ya umurci dansa da ya sanya hannu a kakardan yarjejeniyar a madadinsa, kafin aka bayar da rancen kuɗaɗen ga wanda ake kara.
Lauyan ya kuma shaida wa kotu cewar bayan da wanda ake ƙara ya dawo Najeriya ya sanya hannu da kansa a wata takardar yarjejeniyar ta daban da shi mai karar.
Ya ce, yarjejeniyar ta ginu ne akan za a biya bashin bayan wata shida, amma tun da aka bayar a shekarar 2018 bai biya ba har aka zo gaban kotun.