Kotu ta ba da umarnin tsare tsohuwar Minista Sadiya Umar Farouq

Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq na fuskantar zargin badakalar Dala miliyan 1.3 da kuma Naira miliyan 746.6.

Kotu ta ba da umarnin tsare tsohuwar Minista Sadiya Umar Farouq

Babbar Kotun Abuja Kotu ta ba da umarnin tsare tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq kan zargin karkatar da Dala miliyan 1.3 da kuma Naira miliyan 746.6 zuwa aljihunsu.

Kotun ta kuma ta ba da umarnin kamo tsohon Babban Sakataren ma’aikatar, Alkali, kan kin halartar zamanta na ranar Alhamis.

Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ce ta yi karar su a kotun bisa wasu tuhume-tuhume 21.

Hukumar tana zargin Sadiya da Alkali da mutum ne uku da karkatar da kuɗaɗen zuwa aljihunsu bayan an samu rarar kuɗin daga shirin aikin rajistar ɗaukin gaggawa ya ƙasa.

Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) za ta gurfanar da mutanen su uku a gaban Mai shari’a Jude Onwuegbuzie, bisa zargin laifuka guda 21 da suka shafi cin amanar ƙasa da kuma cin zarafin ofis.

Haka kuma, ana tuhumar su ne da bayar da kwangila ta hanyar zamba da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai kusan $1,300,000 (Dalar Amurka miliyan ɗaya da dubu ɗari uku) da kuma N746,574,303, a lokacin da suke jagorantar ma’aikatar.

Kashi na farko na tuhumar ta ce: “Sadiya Umar Farouƙ, sa’ilin da kike Ministar Harkokin Jinƙai, da Bashir Nura Alkali sa’ilin da kake Babban Sakatare na Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, tsakanin 8 ga Mayu, 2021 zuwa 22 ga Satumba, 2022, a Abuja, a cikin ikon wannan Kotu mai daraja, kuma a matsayinku na waɗanda aka amince wa da wasu kadarori, wato jimillar kudi har $1,300,000.00, kun aikata laifin cin amanar ƙasa game da waɗancan kadarori lokacin da kuka karkatar da kuɗaɗen don amfanin kanku ta hanyar zamba.

Waɗannan kuɗaɗe an yi nufin a mayar da su ne zuwa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai daga kamfanin ɓisual ICT Limited, kasancewar kuɗaɗen rarar da ma’aikatar ta biya a ƙarƙashin Ofishin Gudanar da Tsaro na Kasa (NASSCO) don tantance masu cin gajiyar shirin Rapid Response Register. Ta hakan kun aikata laifi saɓanin sashi na 315 na kundin hukunta manyan laifuka (Penal Code).”

Lauyan mai gabatar da ƙara, Rotimi Jacobs (SAN), ya sanar da kotun cewa an shigar da ƙarar ne tun ranar 15 ga Disamba, 2025, amma ba a samu damar miƙa wa wanda ake ƙara na ɗaya da na biyu takardar sammacin kotu ba.

“Ba mu samu damar gurfanar da su ba a ranar 15 ga Disamba, saboda ba mu samu damar gabatar da su ba, amma lauyoyinsu a kotu sun yi alƙawarin cewa za su gabatar da waɗanda ake ƙarar, amma ba mu gan su ba har sai da mai shari’a ya ba da umarnin miƙa sammacin ta hannun jami’an tsaro.”