Kotu ta ba DSS umarnin sakin Godwin Emefiele

Kotun ta bayyana kamawa da tsare Emefiele a matsayin haramtaccen lamari.

Kotu ta ba DSS umarnin sakin Godwin Emefiele

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin gaggauta sakin dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da ke tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS.

Kotun ta ce kamawa tare da tsare dakataccen gwamnan Babban Bankin da DSS ke yi ya saɓa wa doka.

Yayin da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bello Kawu ya ce kamawa da kuma bincikar Mista Emefiele, ya saɓa wa hukunci da kuma umarnin da wata kotun ta bayar na sakin sa.

Lauyan Emefiele, Peter Abang, ya nemi kotun da ta jingine sannan ta ayyana kamu tare da tsare shin da hukumar DSS ke yi a matsayin haramtacce.

Kasancewar a ranar 29 ga watan Disamban 2022 wata kotu ta dakatar da kama Mista Emefiele.

Aminiya ta ruwaito cewa a Alhamis din da ta gabata ce DSS ta ce ta gurfanar da Godwin Emefiele a gaban kotu.

Wannan ya biyo bayan umarnin da wata Babbar Kotu a Abuja ta bayar ranar Alhamis cewa ko dai DSS ta gurfanar da shi cikin mako guda ko kuma ta sake shi.

’Yan sa’o’i bayan wannan umarnin ne, kakakin DSS, Peter Afunanya ya ce an gurfanar da Emefiele bisa biyayya ga umarnin kotun.

Sai dai bai bayyana kotun da aka gurfanar da shi ba ko tuhumar da aka yi masa gaban kotun.

Ana iya tuna cewa, a ranar Juma’a 9 ga Yunin 2023 ne Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga muƙaminsa na Gwamnan Babban Bankin Kasa.

Washegari kuma DSS ta sanar da cewa Mista Emefiele ya shiga hannunta.

Sai dai babban lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, ya shawarci DSS ta bar EFCC ta gurfanar da Emefiele gaban kotu kasancewar ana zarginsa ne da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

Mista Falana ya ce kamata ya yi da zarar DSS ta kammala bincike ta tura Mista Emefiele zuwa ga EFCC.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa