Kotu ta ba wa Moh’d Abacha takarar Gwamnan Kano a PDP

Hakan na nufin kotun ta kori takarar Sadiq Wali

Kotu ta ba wa Moh’d Abacha takarar Gwamnan Kano a PDP

Mohammed Sani Abacha

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha a matsayin halastaccen dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Hakan dai na nufin kotun ta soke takarar Sadiq Aminu Wali wanda a baya aka tabbatar a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Da yake yanke hukuncin ta intanet ranar Alhamis, Alkalin kotun, Mai Shari’a A. M. Liman, ya soke zaben fid-da gwanin da ya samar da Sadiq Wali a matsayin dan takarar Gwamnan na Kano a PDP.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta maye gurbin Sadiq din da Mohammed Abacha.

Tun da farko dai an shirya yanke hukuncin ne da misalin karfe 12:00 na ranar ta Alhamis, amma daga bisani aka daga zuwa karfe 5:00 na yamma, sannan aka yanke shi da misalin karfe 5:30.

Kotun dai ta amince da dukkan bukatun masu shigar da karar.

Mohammed Abacha dai maka INEC ne a gaban kotun Sadik Wali da kuma Shugaban PDP na Kano, Shehu Wada Sagagi.

Idan za a iya tunawa, tsagin jam’iyyar PDP guda biyu lokacin da take fama da rikici a Jihar sun shirya zabukan fid-da gwani guda biyu, lamarin da ya sa aka samu ‘yan takarar guda biyu, kuma kowanensu ke ikirarin shi ne halastacce.

Ko a karshen makon da ya gabata sai da wasu suka yi taron bayar da tuta ga Sadiq Wali, kodayake daga bisani Shugaban jam’iyyar, Sagagi, ya ce ba da yawunsu aka yi ba.