Kotu ta bada umarnin maidawa Dasuki fasfonsa
Wata babbar kotu da ke yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja, ta bada umarnin a maidawa tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki, fasfonsa don ba shi damar fita kasar waje ganin likitansa. Kotun karkashin Mai shari’a Hussein Baba-Yusuf ce ta umarci magatakardan kotun da ya maidawa Dasuki fasfo din ta hannun […]
Sambo Dasuki
Wata babbar kotu da ke yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja, ta bada umarnin a maidawa tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki, fasfonsa don ba shi damar fita kasar waje ganin likitansa.
Kotun karkashin Mai shari’a Hussein Baba-Yusuf ce ta umarci magatakardan kotun da ya maidawa Dasuki fasfo din ta hannun lauyansa domin sabunta takardar saboda wa’adinsa ya riga ya cika tun bayan da kotu ta kwace fasfo din.
Wannan umarnin kotun zai bai wa Dasuki damar samun biza zuwa asibiti ganin likitansa bayan shekara hudu da ya yi tsare.
Ba na takun saka da kowa – Sambo Dasuki
Sambo Dasuki ya musanta fallasa wa EFCC abokan hadin bakinsa