Kotu ta bai wa El-Rufai izinin ganin likita a Abuja
Kotun ta jaddada cewa duk zirga-zirgar da za a yi da tsohon gwamnan za ta kasance ƙarƙashin kulawar ICPC.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta bai wa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, izinin zuwa ganin likita a wasu asibitoci da ke Abuja domin duba lafiyar idanunsa da haƙoransa.
Hukumar Yaƙi da Rashawa ICPC ta bayyana cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan lauyoyin El-Rufai sun roƙi a ba shi damar samun kulawar lafiya.
- An ɗaure matashi rai-da-rai kan yi wa yarinya fyaɗe a Kalaba
- Maniyyatan Najeriya 6,000 sun isa ƙasa mai tsarki
Mai magana da yawun ICPC Okor Odey ya ce kotun ta umarci hukumar da ta riƙa raka El-Rufai ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro zuwa Mile Dental Clinic da Skipper Eye-Q Hospital a Abuja duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, sannan a dawo a ci gaba da tsare shi bayan ya gama ganin likitoci.
Kotun ta jaddada cewa duk zirga-zirgar da za a yi da tsohon gwamnan za ta kasance ƙarƙashin kulawar ICPC.
Ana tuhumar El-Rufai da laifukan zamba da halasta kuɗaɗen haram, amma ya musanta zarge-zargen da ake masa.