Kotu ta bai wa Gwamna Masari nasara akan PDP

Kotun sauraron kararrakin zabe wadda jam’iyyar PDP ta shigar da kara inda ta kalubalancin zaben Gwamna Masari, a yau kotun ta tabbatar da nasarar Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari a zaben 2019 da ya gabata. Kotun wacce alkalai uku suka yi hukunci, an samu rinjayen alkalai biyu kan daya. Inda biyu suka kori karar, […]

Kotu ta bai wa Gwamna Masari nasara akan PDP

Gwamna Jihar Katsina Aminu Bello Masari

Kotun sauraron kararrakin zabe wadda jam’iyyar PDP ta shigar da kara inda ta kalubalancin zaben Gwamna Masari, a yau kotun ta tabbatar da nasarar Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari a zaben 2019 da ya gabata.

Kotun wacce alkalai uku suka yi hukunci, an samu rinjayen alkalai biyu kan daya. Inda biyu suka kori karar, daya kuma ta soke zaben gaba dayansa.

Mai Shari’a Hadiza Ali Jos, ita ce ta ce, ta soke zaben Gwamna Masari saboda bai cancanci zama dan takara ba, kuma ta bada umarni a sake zabe cikin kwana casa’in ba tare da Masari ya shiga zaben ba.

Sai dai kuma mai shari’a E.B Omotoso da kuma mai shari’a A.I Ityonyiman, suka ce sun kori wannan kara saboda rashin cancantar karar kuma sun tabbatar da Masari a matsayin gwamnan jihar Katsina.