Kotu ta bai wa gwamnati hurumin mallakar kadarorin Tsohuwar Minista

Babbar kotun tarayya da ke yin zamanta a Jihar Legas ta bayar da ummarnin cewa gwamnatiin  tarayya na da damar mallakar kadarori 56 da ake zargin Tsohuwar Ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ta mallaka tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013 na fiye da Naira biliyan uku. Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdulaziz Anka shi ya bayar da […]

Kotu ta bai wa gwamnati hurumin mallakar kadarorin Tsohuwar Minista

Babbar kotun tarayya da ke yin zamanta a Jihar Legas ta bayar da ummarnin cewa gwamnatiin  tarayya na da damar mallakar kadarori 56 da ake zargin Tsohuwar Ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ta mallaka tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013 na fiye da Naira biliyan uku.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdulaziz Anka shi ya bayar da ummarnin jiya yayin da yake yanke hukunci kan bukatar da Hukumar EFCC ta shigar na neman kotun ta baiwa gwamnatin tarayya damar mallakar kadarorin Ministan.
A hukuncin da ya yanke, Alkalin ya ummarci Hukumar EFCC ta baiwa wani kamfani kwangilar lura da kadarorin tare da baiwa wacce ake kara kwanaki 14 ta bayyana dalilanta na kin mallaka wa gwamnatin tarraya kadarorin.
Hukumar EFCC ta mika jerin sunayen wadanda take kara wadanda suka hada da ita kanta Diezani, da Donald Chidi Amamgbo da wasu kamfanoni hudu da suka hada da Kamfanin da ke Lura da gidaje na Chapel Properties da Kamfanin rukunin Gidaje na Blue Nile da Kamfanin Azinga Meadows da kuma wani kamfani mai suna Vistapoint.