Kotu ta bai wa Gwamnatin Kano umarnin sakin Kwamishinan Ganduje
Gwamnatin Kano na zargin tsohon Kwamishinan da almundahanar naira biliyan ɗaya.
Mai Shari’a S. A Amobeda na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ya bayar da umarnin sakin tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Idris Wada Saleh wanda ake zargi da almundahanar naira biliyan ɗaya.
Aminiya ta ruwaito cewa a baya-bayan nan ne babbar kotun Majistaren jihar ce ta bayar da umarnin tsare shi a hannun hukumar yaki da rashawa da karɓar korafe-ƙorafe ta jihar (PCACC).
- Abubuwan da suka kamata a sani kan cutar Diphtheria da take yaduwa a Najeriya
- Yadda nakasassu da tsofaffi suka yi aikin Hajji bana
An zargin tsohon kwamishinan da yaudara da kuma yin karya a takardun wasu ayyuka
Hukumar yaki da rashawa ta jihar ta yi zargin cewa a shekarar 2023, tsohon kwamishinan ya bai wa kamfanin Arafat construction da kamfanin ‘Multi Resources’ kudi nairan biliyan ɗaya domin gyaran tituna 30 a cikin birnin jihar.
To sai dai hukumar yaki da rashawar ta ce babu ko ɗaya daga cikin aikin da aka yi.
A baya-bayan nan dai hukumar PCACC ta ce ta aike da takardar gayyata ga tsohon Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje kan ‘bidiyon dala’.
To amma Babbar Kotun Tarayya a jihar ta dakatar da hukumar daga gayyatar tsohon gwamnan, har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron ƙorafin da Gandujen ya shigar gabanta yana neman ta hana hukumar bincikensa.