Kotu ta bayar da belin da tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan
Magoya bayan nasa da dama na kallo kamen a matsayin cinne na siyasa.
Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan ya koma gidansa da ke Lahore a ranar Asabar bayan da wata kotu a Islamabad ta bayar da shi beli.
Wannan dai ya biyo bayan kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnati mai ci wanda ya tsananta a makon jiya.
- An fatattaki Southampton daga Firimiyar Ingila bayan shekara 11
- An ba da umarnin kama dan marigayi Fela, Seun Kuti
Sai dai gwamnatin ta sha alwashin sake kame Khan idan aka sake shi, lamarin da ake fargabar zai sake rura wutan rikici a kasar.
An dai sako jagoran ’yan adawan kasar ne bayan ya kwashe kwanaki a hannun jami’an ’yan sanda sakamakon zargin da ake masa na cin hanci da rashawa.
A ranar Talatar da ta gabata ce, jami’an tsaro suke tsare Khan, lamarin da ya haifar da tarzoma a wasu sassan kasar tsakanin magoya bayansa da kuma jami’an tsaro.
Lamarain dai ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane kimanin 10 yayin da wasu daruruwa ciki har da jami’an ’yan sanda suka jikkata.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda dubban magoya bayansa suka yi masa maraba tare da yin bikin sako jagoran nasu da yin wasanni da kade-kade da kuma raye-raye.
Magoya bayan nasa da dama na kallo kamen a matsayin cinne na siyasa.