Kotu ta bayar da belin Dani Alves kan Dala miliyan ɗaya

Kotun ta ɗora wa Alves dokar hana shi zuwa kusa da wadda ya aikata laifin kanta, da tazarar mita 1,000.

Kotu ta bayar da belin Dani Alves kan Dala miliyan ɗaya

Wata Kotun Sifaniya ta bayar da belin tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Brazil da kuma Barcelona, Dani Alves kan dala miliyan 1.1.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da cewa Alves zai ajiye fasfo ɗinsa na Brazil da na Sifaniya, domin gudun ka da ya fice daga Sifaniyar.

A ranar Laraba ne Kotun da ke Barcelona ta ce za a iya sakin Dani Alves daga gidan yari kan belin dala miliyan 1.1, yayin da yake ɗaukaka kara kan shari’ar da ake masa ta aikata fyaɗe, bayan ya yi zaman kusan kwatan wa’adin shekaru huɗu na hukunci.

Haka nan kuma, kotun ta ɗora wa Alves dokar hana shi zuwa kusa da wadda ya aikata laifin kanta, da tazarar mita 1,000.

Tun a watan Janairun 2023 dai aka tsare tsohon ɗan wasan baya na Barcelona da Juventus da PSG a wani gidan yari na Barcelona.

Sai kuma a ranar 22 ga watan Fabarairun bana ne aka yanke wa Alves hukuncin kan laifin yi wa wata mata fyaɗe a banɗakin wani gidan rawa na Barcelona a 2022, kuma aka umarce shi ya biya ta Euro dubu 150,000.

Sai dai ya ɗaukaka ƙara kan hukunci, kasancewar hukuncin ba shi ne na ƙarshe ba.