Kotu ta bayar da belin Dokta Bashir Kurfi

Dokta Kurfi ya yi zargin cewa gwamnatin Katsina ta ɗauki nauyin kai wasu wasu shugabannin ’yan bindiga aikin Hajjin bana.

Kotu ta bayar da belin Dokta Bashir Kurfi

Babbar Kotun Majistare ta II da ke Katsina ta bayar da belin Dokta Bashir Kurfi, bayan gurfanar da shi kan zargin ɓata sunan gwamnatin Jihar Katsina.

Ana dai tuhumar Dokta Kurfi, wanda masani ne kan harkokin tsaro kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, da laifuffuka biyu da suka shafi ɓata suna da yaɗa bayanan da ake zargin ƙarya ne.

Lamarin na zuwa ne bayan wata hira da ya yi da Trust TV a ranar 24 ga Yunin 2026, inda ya yi zargin cewa gwamnatin Katsina ta ɗauki nauyin kai wasu wasu shugabannin ’yan bindiga aikin Hajjin bana.

Sai dai Dokta Kurfi ya musanta zarge-zargen, lamarin da alƙalin kotun, Zaharaddeen Sani, ya bayar da  belinsa kan kuɗi Naira 500,000 tare da sharaɗin gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, waɗanda dole ne su mallaki gidaje a cikin birnin Katsina.

Kotun ta kuma ce mutanen biyu da za su tsaya masa dole ne a ci tararsu kowannensu Naira 500,000 idan wanda ake tuhuma ya tsere ko ya gaza halartar zaman kotu na gaba.

Aminiya ta ruwaito cewa an ɗage shari’ar zuwa ranar 13 ga Agustan 2026 domin fara sauraren shaidu.

Lauyan Dokta Kurfi, A.D. Umar, ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa kotu za ta wanke wanda yake karewa bayan kammala shari’ar.