Kotu ta bayar da belin Emefiele kan Naira miliyan 50
A makon da ya gabata ne, EFCC ta sake gabatar wa kotu wasu sabbin tuhume-tuhume 26 a kan Emefiele.
Babbar Kotu da ke zamanta a birnin Ikeja na Jihar Legas, ta bayar da belin Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan kuɗin Naira miliyan 50.
Mai shari’a Rahman Oshodi ne, ya bayar da belinsa a kan kuɗi Naira miliyan 50 tare da buƙatar gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa.
- Ya hallaka budurwarsa da wuƙa kan cacar-baki
- Titin Legas-Kalaba: Duk kilomita 1 za ta laƙume 4bn — Minista
Kotun ta kuma ce waɗanda za su tsaya masa dole ne su kasance suna da shaidar biyan gwamnatin Jihar Legas haraji na tsawon shekara uku.
Mai shari’a Oshodi, ya ce dole ne mutanen su kasance suna da sauran duk wasu takardu da za a buƙata kafin bayar da belin Emefiele.
Alƙalin kotun ya kuma ce ya gamsu da sharuɗan belin Naira miliyan ɗaya, wanda kotun ta bai wa takwaran Emefiele, Henry Isioma-Omoil wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Olufunke Sule-Hamzat na babbar kotun Legas da ke Yaba.
A cewar kotun, dole ne a kai takardun belin zuwa kotun laifuka ta musamman tare da yi musu rajista a ƙarƙashin tsarin kula da beli na Jihar Legas.
A makon da ya gabata ne, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta sake gurfanar da Emefiele a gaban kotu kan wasu sabbin tuhume-tuhume 26 da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa.