Kotu ta bayar da belin Fayose
Alkalin Kotun Tarayya da ke zama a Jihar Legas, Mojisola Olatoregun ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose. Alkalin ta bayar da belin ne a kan Naira miliyan 50 wanda wadanda za su tsaya masa guda biyu za su ajiye a bankuna biyu masu girma sannan kuma wadanda suke da shaidar biyan […]
Alkalin Kotun Tarayya da ke zama a Jihar Legas, Mojisola Olatoregun ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose.
Alkalin ta bayar da belin ne a kan Naira miliyan 50 wanda wadanda za su tsaya masa guda biyu za su ajiye a bankuna biyu masu girma sannan kuma wadanda suke da shaidar biyan haraji na shekara uku.
Hakanan kuma ta umarci gwamnan da ya ajiye takardar fita kasar wajensa a kotun.
Tun farko, lauyan Fayose, Kanu Agabi ne ya bukaci kotun ta bayar da belin Fayose a matsayinsa na tsohon gwamnan, sannan duba da cewa da kansa ya kawo kansa ofishin na EFCC.
Amma sai alkalin EFCC ya nuna rashin amincewarsa da hakan, inda ya ce Fayose din duk da ya kawo kansa, amma ya zo da ‘yan ta’adda ofishin hukumar.
Ana dai zargin Fayose ne laifuka 11 wadanda suka hada da zanba cikin aminci da sauransu da suka kai jimillar kudi Naira biliyan 2.2.