Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da ’yarsa kan N200m
Za a tura su a gidan gyaran hali muddin suka saba wa ɗaya daga cikin sharuɗan beli.
A wannan Alhamis ɗin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya gurfana a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin badaƙalar Naira biliyan biyu.
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa a Nijeriya ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun da ke Maitama a Abuja.
Aminiya ta ruwaito cewa, EFCC ta sanar da cewa za ta gurfanar da Sirika a gaban kuliya tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ‘yarsa Fatima; Jalal Hamma da Al-Duraq Investment Ltd, bisa zargin badaƙalar kuɗi da ta kai Naira biliyan 2.7.
Ga wasu hotunan isowarsu kotu.
Tuni dai Babbar Kotun ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen saman da ‘yarsa Fatima waɗanda aka gurfanar da su yau a gaban kotu.
An bayar da belin ne kan kuɗi naira miliyan 100 ga kowannen su, har da ma sauran mutum biyu da aka gurfanar tare da su.
Sauran ka’idojin belin sun hada da kawo waɗanda za su tsaya musu waɗanda suka mallaki kadarori a Abuja.
Haka kuma, a ƙunshin ka’idojin, kotun ta haramta wa waɗanda ake tuhuma fita ƙetare ba tare da izininta ba.
Kotun ta kuma gargaɗi duk waɗanda ake tuhumar da cewar za a garkame su a gidan gyaran hali muddin suka saba wa ɗaya daga cikin sharuɗan belin da ta gindaya.