Kotu Ta Bayar Da Belin Murja Kunya

Kotun ta gindaya wa fitacciyar jarumar TikTok ɗin sharuɗa biyu kafin ta bayar da belinta.

Kotu Ta Bayar Da Belin Murja Kunya

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Unguwar Bompai ta Jihar Kano ta bayar da belin fitacciyar jarumar TikTok da aka kama kan zargin ɓata tarbiyya, Murja Ibrahim Kunya.

Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Saminu ta sanya ƙa’idojin da za a cika kafin a bayar da belin Murna, daga ciki za a ba da kuɗi Naira dubu ɗari biyar.

Haka kuma kotun ta umarce ta da ta kawo mutanen da za su tsaya mata guda biyu.

Kotun ta ce dole ne ɗaya ya kasance dan uwanta na kusa, yayin da ɗayan kuma zai kasance wanda ya mallaki kasa mai daraja a Jihar Kano.

Idan ba a manta ba Hukumar HISBAH ce ta miƙa Murja ga kotu domin bincike da ɗaukar mataki muddin an sameta da laifin da ’yan unguwarsu suka kai kararta.

Kamun Murja Kunya ya janyo ce-ce-ku-ce wanda wasu ke ganin yana da nasaba da abin da ya janyo Kwamandan HISBAH Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus ɗin kashin kai a kwanakin baya, kafin daga bisani a daidata shi da Gwamnatin Kano ya koma bakin aiki.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS