Kotu ta ba da belin Sowore a kan N200m

Kotun ta kara da cewa cewa wajibi ne mutanen da za su tsaya wa Sowore su samu tantancewar lauyoyin  masu gabatar da kara, Akinlolu Kehinde, (SAN)

Kotu ta ba da belin Sowore a kan N200m

Omoyele Sowore

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta bayar da belin dan gwagwarmaya, kuma mai kafar yada labarai ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a kan kudi Naira miliyan 200.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ce ta gurfanar da Sowore a gaban kotu, kan zargin cin mutuncin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, inda bayyana shi a matsayin “babban mai laifi” a wani sako da dan gwagwarmayan ya wallafa a shafukansa na X da Facebook.

The defendant’s lawyer, R. O. Adakole, however, appealed to the judge that Sowore be released to him to enable him get his passport from the US embassy in Lagos.

Justice Umar then adjourned to July 6, 2026, for continuing of hearing after Sowore’s counsel plea.

 

A safiyar Talatar nan ce Mai Sharia Umaru Mohammed ya bayar da belin Sowore—dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar AAC— da sharadin ya kawo mutum biyu da za su tsaya masa.

Alkalin ya shardanta cewa wajibi ne daya daga cikin masu tsayawar ya kasance basaraken gargajiya daga garinsu Sowore da ke Karamar Hukumar Ese-Odo da ke Jihar Ondo. Mutum na biyu kuma, wajibi ne ya kasance ya mallaki gida a Abuja.

Kotun ta kara da cewa cewa wajibi ne mutanen da za su tsaya wa Sowore su samu tantancewar lauyan masu gabatar da kara, Akinlolu Kehinde, (SAN).

Wajibi ne kuma wanda ake zargin, wato Sowore, ya mika takardar fasfon tafiye-tafiyensa ga kotun, kafin a yi komai.

Lauyan wanda ake zargi, R. O. Adakole, ya bukaci kotun ta bayar da izinin sakin Sowore domin ya karbo fasfo dinsa daga Ofishin Jakadancin Amurka da ke Legas.

A karshen zaman, alkalin ya dage sauraron batun zuwa ranar 6 ga watan Yuli, domin sauraron rokon lauyan Sowore.

a ranar 16 ga Yuni, kotun ta bayar da umarnin tsare Omoyele Sowore, a gidan gyaran hali na Kuje, bayan Mai Shari’a Mohammed Umar ya soke belin da ya ba shi a watan Disamba da ya gabata.

Bayan haka, alƙalin ya bayar da umarnin kama shi, sakamakon kin bayyana a kotu domin ci gaba da shari’arsa kan zargin laifukan damfara ta intanet da kuma bata suna.

A makon jiya, Mai Shari’a Umar ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Sowore a gidan yarin Kuje har sai an yanke hukunci kan buƙatarsa na dakatar da soke belin da aka yi da kuma umarnin kama shi.

Da shari’ar ta ci gaba a ranar Talata, alƙalin ya yi watsi da wata buƙata ta Sowore da ke neman a cire alkalin daga ci gaba da jagorantar shari’ar bisa zargin nuna son kai.