Kotu ta bayar da belin ’yar kasar China
Babbar kotun tarayya ta Ibadan ta bayar da belin wata ’yar kasar China, mai suna Zhou Jun, wacce aka tsare ta a gidan yari tsawon kwanaki 14, bisa zargin laifin damfarar Naira miliyan 35 da dubu 600 mallakar Awokson Dilan Shem da Abdullahi Sani Maiyanchi da Abdulrahman Mohammed, wadanda kamfaninsu mai suna Tonjons ya kulla […]
Babbar kotun tarayya ta Ibadan ta bayar da belin wata ’yar kasar China, mai suna Zhou Jun, wacce aka tsare ta a gidan yari tsawon kwanaki 14, bisa zargin laifin damfarar Naira miliyan 35 da dubu 600 mallakar Awokson Dilan Shem da Abdullahi Sani Maiyanchi da Abdulrahman Mohammed, wadanda kamfaninsu mai suna Tonjons ya kulla yarjejeniyar sayar da ma’adinai ga wannan mata da wani dan uwanta, mai suna Mista Sheng, wanda ake nema ruwa a jallo.
Alkalin kotun, mai shari’a Emmanuel Ayo, ya bayar da belin matar ne a kan Naira miliyan biyu da mutane biyu, wadanda suka tsaya mata, kuma dole su kasance sun mallaki sanannun kamfanoni da asusun ajiya a banki. Sannan ita wannan mata dole ne ta mika wa kotun katin fasgo dinta.
Alkalin ya ce ya amince da bayar da belin Zhou Jun ne, saboda lura da ya yi cewa, kashi 99 cikin 100 na laifuka 16 da ake tuhumarta an aikata su ne tun cikin shekara ta 2011, wanda ba ta yi wani yunkurin tserewa a cikin wannan lokaci ba.
Mai gabatar da kara, Jami’in ’yan sanda, DSP Fawole Bukola, ya sanar da kotun cewa, wannan mata ta mallaki manyan otal-otal a Legas, ta bayar da cakin kudi na Naira dubu dari bakwai, amma na bogi ne ga Mista Awokson Dilan Shem, domin an kasa karbar kudin a bankin Zenith na Ibadan, wanda yin hakan laifi ne da ya cancanci a hukunta wanda ya aikata shi.
Wakilinmu ya ce wannan mata Zhou Jun, ta lullube fuskarta da wani kyalle a lokacin da take saukowa daga cikin motar gidan yari (wato Black Maria). Kuma babu wani daga cikin dangin wannan mata da aka gani a harabar kotun.
Shugaban kamfanin hakar ma’adinai na Tonjons, Mista Awokson Dilan Shem, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Tun farko dan uwan wannan mata, Mista Sheng, shi ne ya taso daga Legas ya zo domin sayen duwatsun alfarma a wajenmu a nan Ibadan, amma a dalilin rashin jin harshen Turanci sai muka dunguma zuwa Legas wajen wannan mata Zhou Jun, wacce ta tsaya masa aka yi ciniki, kuma aka biya mu kudinmu a lokacin da aka yi mana alkawari. Amma a karo na biyu ne da aka sake kulla irin wannan ciniki, wanda wannan mata ta sake tsaya wa dan uwanta muka sayar masa da ma’adinai na fiye da Naira miliyan 35, daga nan ya yi layar zana har zuwa yau din nan ba a gano maboyarsa ba.”
Alhaji Abdullahi Sani Maiyanchi, shi ne ya mallaki kaso mafi yawa na Naira fiye da miliyan 11 daga cikin jimlar kudin da wadannan ’yan kasar China suka damfare su, kamar yadda ya bayyana wa Aminiya. “Tun da na fara wannan sana’a shekaru 30 da suka wuce, ban taba fadawa cikin irin wannan masifa ba. Amma na mika komai ga Allah (SWT) da nake rokon Ya fitar da mu daga cikin wannan matsala. Muna godiya ga sashen binciken manyan laifuka na na ’yan sandan ciki CID da ke Iyaganku a Ibadan, inda mataimakin Kwamishinan ’yan sanda, AC Dasuki Galadanci da suka yi fafutukar kwato mana hakkinmu,”inji shi.