Kotu ta bayar da sammacin kama Alkalin alkalai Onnoghen
Kotun da’ar ma’aikata (CCT) ta bayar da sammacin kama alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen wanda aka dakatar. Babban alkalin kotun ne mai sharia Dandali Umar ya bayar da sammacin kama Alkalin alkalan a jiya Laraba. Danladi Umar ya sanarwa Sufeta Janar na `yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su kama Onnoghen su mika […]
Kotun da’ar ma’aikata (CCT) ta bayar da sammacin kama alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen wanda aka dakatar.
Babban alkalin kotun ne mai sharia Dandali Umar ya bayar da sammacin kama Alkalin alkalan a jiya Laraba.
Danladi Umar ya sanarwa Sufeta Janar na `yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su kama Onnoghen su mika shi ga kotun gobe juma’a 15 ga watan Fabrairu
An da bayar dai bayar da umarnin sammacin kama Alkalin alkalan bayan ya ki gurfana gaban kotun domin kare zargin da ake ma sa.