Kotu ta bayar da umarnin bai wa Hamdiyya tsaro

Lauyan ya yi wannan roƙo ne bayan da ya ce rayuwar matashiyar na cikin hatsari.

Kotu ta bayar da umarnin bai wa Hamdiyya tsaro

A yayin da ake ci gaba da shari’a tsakanin matashiyar nan Hamdiyya Sidi da Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, lauyan Hamdiyya ya roƙi kotu ta bai wa matashiyar jami’an tsaro domin kare rayuwarta.

Lauyan matashiyar, Abba Hikima, ya bayyana cewa rayuwar Hamdiyya na cikin hatsari, wanda hakan ya sa ya roƙi kotu ta ba ta kariya.

Lauyan, ya bayyana hakan ne bayan zaman kotun da aka yi a ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce: “Kotu ta bayar da umarni cewa duk lokacin da za a gudanar da shari’a, za a kawo jami’an tsaro masu makamai domin su ba ta kariya.”

Kotu ta amince da roƙon lauyan kuma ta bayar da umarnin cewa a samar da jami’an tsaro masu riƙe da makamai don tabbatar da cewa Hamdiyya tana samun kariya yayin gudanar da shari’ar.

Aminiya ta ruwaito cewa hukumomi a Jihar Sakkwato, sun kama Hamdiyya bayan ta wallafa wani faifan bidiyo, inda ta soki Gwamnan Sakkwato a shafinta na TikTok.