Kotu ta bayar da umarnin kamo Ado Gwanja
Kotu ta haramta wa Ado Gwanja yin waka har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kansa.
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Sharia Aisha Mahmud, ta ba da umarnin kamo mawaki Ado Isa Gwanja.
Kotun ta kuma haramta wa mawakin yin waka har zuwa lokacin da ’yan sanda za su kammala bincike a kansa.
- Aljeriya ta kaddamar da Masallaci mafi girma a Afrika
- Kotu ta dage sauraron shari’ar Danbilki Kwamanda a Kano
Wannan dai na zuwa ne bayan da Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ta maka Ado Gwanja da wasu kara a kotu, kan amfani da kalaman da ba su dace ba a wakokinsu.
Aminiya ta tuntubi, shugaban Kungiyar Jarumai na Kannywood, Alhassan Kwalle, amma jarumin, ya ce ba shi da masaniya game da umarnin kotun na kamo Ado Gwanja.
Idan ba a manta ba a 2023, kotu ta gayyaci Ado Gwanja, Idirs mai wushirya, Murja Ibrahim Kunya, 442 da wasu bayan da wasu mazauna Kano suka maka su a kotu kan zargin bata tarbiyyar yara.
A baya-bayan nan, Hukumar Hisba ta jihar, ta kama tare da gurfanar da fitacciyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya a kotun Musulunci da ke Unguwar PRP a jihar.
Kotun ta tuhumi Murja da laifin koyar da karuwanci da bata tarbiyya, wanda daga bisani ta tasa keyarta zuwa gidan yari.
Sai dai daga baya labari ya bulla cewar, Murja ta yi layar zana daga gidan yarin, lamarin da ya haifar da cece-kuce, inda wasu ke ganin matashiyar na da uwa a gindin murhu a gwamnati.
A makon da ya gabata ne, kotun ta sake zama kan sauraren shari’ar, inda ta bayar da umarnin yi wa Murja gwajin ƙwaƙwalwa tare da zama karkashin kulawar Hisba har na tsawo wata uku.
A gefe guda guda, matashiyar TikTok Ramlat Mohammed, wadda ta ayyana kanta a matsayin ’yar maɗigo a TikTok, kotun Musulunci a jihar ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari.