Kotu ta biya kudin marayu Naira miliyan 21 da ya makale
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna ta biya Naira miliyan 21 da dubu 600 na gadon marayu iyalan marigayi Alhaji Yahaya Kwana wanda aka zargi wata ma’aikaciyar Kotun Lardi ta Shari’a da ke Kawo Kaduna, Misis Lami Baba Kwasau da sacewa. Aminiya ta ruwaito cewa kudin na gado ne da ya kamata a raba wa ’ya’yan […]
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna ta biya Naira miliyan 21 da dubu 600 na gadon marayu iyalan marigayi Alhaji Yahaya Kwana wanda aka zargi wata ma’aikaciyar Kotun Lardi ta Shari’a da ke Kawo Kaduna, Misis Lami Baba Kwasau da sacewa.
Aminiya ta ruwaito cewa kudin na gado ne da ya kamata a raba wa ’ya’yan marigayin su 17 da matansa biyu da kuma mahaifiyarsa.
Amma a lokacin da ya kamata a raba wa marayun kudinsu sai aka ce wai ma’aikaciyar da aka bukaci ta fito da kudin daga banki ta gudu da su.
Da yake jawabi ga Aminiya lauyan iyalan marigayin Barista Ibrahim Waru ya ce tunda an riga an biya kudin abin da kawai ya rage yanzu shi ne su jira a janye yajin aikin da ma’aikatan kotu ke yi domin a sanar da kotu halin da ake ciki.
“Yanzu haka mun kammala saka hannu a takardun kudin domin aika kudin cikin asusun ajiyar iyalan marigayin da ke bankin Keystone, tuni an aika da wasika dauke da tambarin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna ga Manajan Bankin. Idan an janye yajin aikin ma’aikatan kotu za mu sanar da kotu ci gaban da aka samu domin jiran abin da za ta ce,” inji shi.
Kakakin Hukumar Shari’a ta Jihar, Misis Comfort Sawok ta ce sun amince da sasantawa a wajen kotu ne saboda yarjejeniyar da aka yi tsakanin lauyoyin masu kara da wanda ake kara.
“Dukkan bangarorin biyu sun amince su tattauna a tsakaninsu domin neman mafita, a ofishin Alkalin Alkalai da Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jiha, dukkansu sun amince da matsayar da aka cimma. Wanda ake kara ya biya mai kara Naira miliyan 21 da dubu 644 da 229 da kwabo 06 a matsayin kudin da aka shigar a Kotun Lardi ta Shari’a da ke Kawo, domin a raba wa marayun kuma mai kara ya amince da abin da aka bayar a matsayin hukuncin kotun,” inji ta.
Idan ba a manta ba kusan wata hudu ke nan ake ta ja-in-ja a kan batun wannan kudi da suka yi batan-dabo bayan an shigar da su asusun ajiyar kotu domin raba wa magadan.