Kotu ta bukaci Goodluck Jonathan ya bayyana a gabanta

  Babbar Kotun Abuja ta bayar da kwana biyar ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya bayyana a gabanta, inda zai tsaya a matsayin shaida ga tsohon mai magana da yawun Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh. Mai shari’a Okong Abah ya ce kotun ba za ta zargi tsohon Shugaban kasar ba bisa rashin bayyanarsa a […]

Kotu ta bukaci Goodluck Jonathan ya bayyana a gabanta

 

Babbar Kotun Abuja ta bayar da kwana biyar ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya bayyana a gabanta, inda zai tsaya a matsayin shaida ga tsohon mai magana da yawun Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh.

Mai shari’a Okong Abah ya ce kotun ba za ta zargi tsohon Shugaban kasar ba bisa rashin bayyanarsa a kotun a ranar Laraba da ta gabata.

“Zuwa bayar da shaida na da muhimmanci sosai, don haka muna ba wanda ake zargi shawara da ya dage wajen ganin tsohon shugaban ya zo domin ya bayar da shaida.

“Amma idan bai zo ba, za a canza shi da wani shaidan. Domin wanda ake zargi ne ya kira shi ba kotu ba kamar yadda sashe na 124 na kundin tsarin kotun ya tanadar,” inji shi.

Haka nan kuma kotun ta yi watsi da bukatar da Dasuki ya gabatar, inda ya bukaci kotun ta ajiye maganar cewa sai ya zo ya bayar da shaida a shari’ar. Inda alkalin kotun ya ce idan har aka amince da bukatar Dasuki, to lallai sai an canja shari’ar da babbar kotun Abuja ta yanke a ranar 29 ga watan Satumba, inda ta bukaci Dasuki ya bayyana a matsayin shaida.

Lauyan Dasuki, Ahmed Raji (SAN), ya ce wanda yake karewa yana tsare fiye da shekara biyu ke nan, a kan zargin kudin makamai, don haka bai kamata a gayyace shi ya bayar da wani bayani ba a kan wannan shara’ar.

Amma sai kotun ta ba lauyan EFFC, Sylbanus Tahir, umarni da ya tursasa wa Gwamnatin Tarayya ta kawo Dasuki kotu saboda nemansa da ake yi.

Metuh dai yana fusakantar laifuka guda bakwai ne tare da kamfaninsa Destra Inbestment Ltd. a kan zargin karbar Naira miliyan 400 daga Dasuki.

Kafin alkalin ya daga sauraron karar, sai da ya yi kashedi ga kafafen watsa labarai a kan yada labaran karya kan abin da ya faru a kotun.