Kotu ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya dan jarida miliyan

Wata Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya dan jariya Jones Abiri diyyar Naira miliyan 10 bisa tsare shi da ta yin a shekaa biyu ba bisa ka’ida ba Alkalin kotun, mai shara’a Nnamdi Dimgba, ya ce bai kamata ba Gwamnatin Tarayya ta tsare Mista Abiri bayan ta kira shi ta […]

Kotu ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya dan jarida miliyan
Kotu ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya dan jarida miliyan

Wata Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya dan jariya Jones Abiri diyyar Naira miliyan 10 bisa tsare shi da ta yin a shekaa biyu ba bisa ka’ida ba

Alkalin kotun, mai shara’a Nnamdi Dimgba, ya ce bai kamata ba Gwamnatin Tarayya ta tsare Mista Abiri bayan ta kira shi ta dauki bayansa a shekarar 2016.

“Kamata ya yi bayan an dauki bayansa, sai a kais hi gaban kotu a yi shara’a, sannan a yanke hukunci yadda ya dace.”

Shi dai Jones Abiri tun a watan Agusta na shekarar 2016 yake tsare, har sai da lauyoyi karkashin jagorancin Femi Falana suka kai karar Gwamnatin Tarayya a kan tauye hakkin dan Adam.