Kotu ta ce a kamo Sanata Sankara kan kin halartar kotu
Kotun Majistare ta Ringim a Jihar Jigawa ta ba da umarnin a kamo mata Sanata danladi Sankara da wasu mutum biyu da kotun take tuhuma da laifin kin amsa gayyatar da ta yi musu a kan karar da dan takarar kujerar majalisar jihar da tsohon dan Majalisar Tarayya daga mazabar Buji da Birnin Kudu suka […]

Kotun Majistare ta Ringim a Jihar Jigawa ta ba da umarnin a kamo mata Sanata danladi Sankara da wasu mutum biyu da kotun take tuhuma da laifin kin amsa gayyatar da ta yi musu a kan karar da dan takarar kujerar majalisar jihar da tsohon dan Majalisar Tarayya daga mazabar Buji da Birnin Kudu suka shigar kan tayar da hankalin jama’a.
Wadanda kotun ke nema ruwa a jallo sun hada dan Sanata Sankara Auwalu danladi Sankara da wani matashi mai suna dan Gumel, inda alkalin kotun Majistare Nuhu Dawaki Aminu ya ba da umarnin a kamo su saboda ta nemi su halacci zaman kotun a shekaranjiya Laraba da misalin karfe 9:00 na safe amma suka ki bayyana.
Mai shari’a Nuhu Dawaki Aminu ya ba da umarnin a kama wadannan mutum uku a kuma gabatar da su a gaban kotun a zamanta na gaba wato ranar 4/12/2013.
Lauyan wadanda ake karar Omeyere Morgan ya ce wannan ba sabon abu ne ba, a kotu abu ne da za su yi kokarinsu wajen sasantawa tsakanin wadanda ake karar da wadanda suka yi karar.
karar ta biyo bayan zaben cike gurbi na dan majalisar jiha na karamar Hukumar Ringim wanda sakamakon zaben aka samu tashin hankali har aka kama matasa 53 da ake zargi da tada hankalin mutane a kauyen Sankara, inda suka Sassari mutane da adduna ciki har daa Alhaji Farouk Adamu Aliyu, inda aka kwantar da wasu da dama a asibitin Ringim da Kano.