Kotu ta ce a rataye matar Sarki a Nasarawa
Aranar Talatar da ta gabata ce, Alkalin Babbar Kotun ta 2 da ke Lafiya a Jihar Nasarawa, Mai shari’a A’isha Bashir ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga matar marigayi Sarkin Mama da ke Karamar Hukumar Wamba, Alhaji Adamu Zubairu wato Hajiya Amina Zubairu bisa samunta da laifin kashe mijinta ana gobe daurin […]
Aranar Talatar da ta gabata ce, Alkalin Babbar Kotun ta 2 da ke Lafiya a Jihar Nasarawa, Mai shari’a A’isha Bashir ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga matar marigayi Sarkin Mama da ke Karamar Hukumar Wamba, Alhaji Adamu Zubairu wato Hajiya Amina Zubairu bisa samunta da laifin kashe mijinta ana gobe daurin aurensa da amaryarsa a watan Fabrairun shekarar 2014.
Da take yanke hukuncin, Mai shari’ar ta ce bayan kotu ta yi nazarin laifin da ake tuhumar Hajiya Amina Zubairu, wanda a cewarta ya saba wa sashe na 221 na Final Kod. Ta ce “Wannan ba karamin laifi ba ne, laifi ne babba don ya shafi kisa kuma hujjojin da mai shigar da karar ya gabatar ga kotu sun gamsar da ita kuma sun kawar da dukan shakku da kotu ke da su a kan batun. Saboda haka dole ne mai laifi ta fuskanci hukunci mai tsanani.”
Marigayi Alhaji Adamu Zubairu kafin ya gamu da ajalinsa a watan Fabrairun 2014, shi ne Sarkin Mama da ke yankin Kwara a Karamar Hukumar Wamba.
Da yake tsokaci game da hukuncin, lauyan mai kara Barista Jibrin Aboki ya yaba wa matakin da kotun ta dauka, inda ya ce ba shakka hakan zai kasance darasi ga ire-iren Hajiya Amina da ke kashe rayukan ’yan Adam a kan abubuwa da ba su taka kara sun karya ba.
A nasa bangaren, babban dan marigayi Sarkin, Malam Abdullahi Zubairu ya yaba wa hukuncin, ya kuma ce yanzu shi da sauran iyalan mamancin baki daya burinsu ya cika, kasancewar sun sha alwashin tabbatar da kotu ta bi musu hakkinsu, tunda aka kashe mahaifinsu ta hanyar zuba masa guba a abinci. Ya ce ba shakka hukuncin ya gamsar.
Sai dai a bangaren, lauyan wacce aka yanke wa hukuncin, Shekama Shitu ya bayyana wa wakilinmu rashin gamsuwarsa da hukuncin kotun, inda ya ce za su daukaka kara zuwa kotun gaba.