Kotu ta ce wa mutum shi matacce ne duk da ya gurfana gabanta
Wata kotu a kasar Romaniya ta shaida wa wani mutum cewa shi matacce ne a shari’ance duk da yana raye kuma ya gurfana a gabanta cikin koshin lafiya. Mutumin mai shekara 63, mai suna Constantin Reliu ya bace ne a shekarar 2003, sai matarsa ta je kotun ta nemi takardar shaidar cewa mijinta ya rasu […]
Wata kotu a kasar Romaniya ta shaida wa wani mutum cewa shi matacce ne a shari’ance duk da yana raye kuma ya gurfana a gabanta cikin koshin lafiya.
Mutumin mai shekara 63, mai suna Constantin Reliu ya bace ne a shekarar 2003, sai matarsa ta je kotun ta nemi takardar shaidar cewa mijinta ya rasu bayan da ya yi balaguro zuwa kasar Turkiya amma ba tare da sake samun labarinsa ba. Amma a bana kwatsam sai hukumomin Turkiyya suka dawo da shi Romaniya a kan dole, inda ya aka sanar da shi cewa ya riga ya rasu da dadewa, kuma babu abin da za a iya yi domin hukuncin kotun ne na karshe duk da cewa a bayyane yana raye.
Abin mamakin shi ne yadda kotun ta dage kai-da-fata cewa lallai fa Constantin Reliu matacce ne a wajenta duk da cewa ya halarci kotun da kansa kuma cikin koshin lafiya, domin a cewarta tuntuni ta bayar da takardar shaidar cewa ya rasu ga matarsa.
Rahotanni sun ce bayan Reliu ya dawo, kuma ya samu labarin abin da ke faruwa, sai ya je kotun inda ya bukaci ta janye takardar shaidar mutuwarsa da ta bayar, amma kotun ta ce dole ya hakura ya ci gaba da zama a matsayin matacce saboda lokaci ya riga ya kure masa. Reliu ya sanar da kafofin watsa labarai na kasar cewa, “Ni matacce a rubuce duk kuwa da cewa ina raye kuma ina cikin koshin lafiya. Yanzu haka ina fama da talauci, amma kuma tunda ina a matsayin matacce ne yanzu, babu wani abin da zan iya yi.”
An ce Reliu ya bar Romaniya ce da nufin neman aiki a wata kasar a 1992, amma tunda ya dawo a 1999 daga kasar Turkiya, sannan ya koma, tun wancan lokacin iyalansa ba su sake jin duriyarsa ba, sai matarsa ta je kotu ta karbi takardar shaidar cewa ya rasu bayan ta ji shiru.
Da take jawabi a kotun, matar Reliu ta ce ta yi tsammanin cewa mijinta ya rasu ne a wata girgizar kasa da aka yi a kasar Turkiya, wanda hakan ya sa ta je ta karbi takardar shaidar rasuwarsa a kotu. Kuma ta karbi takardar shaidar ce domin ta samu damar sake aure.
Amma duk abin da ake ciki Mista Reliu bai sani ba, sai bana da takardunsa suka daina aiki, kuma jami’an kasar Turkiya suka kama shi suka tilasta masa dawowa Romaniya. Isowarsa ke wuya, jami’an shigi-da-fici na Romaniya suka yi kama shi inda suka ce masa a wajensu ya riga ya rasu tun a shekarar 2003.
Reliu wanda ya nuna cewa yana so ya sake komawa Turkiya domin ya riga ya kafa harkokin kasuwanci a can, yana fama da kalubale babba na yadda zai dawo da matsayinsa, da kuma takardun tafiya. Yanzu haka yana cikin tsaka-mai-wuya domin wannan hukuncin shi ne na karshe.