Kotu ta ce ’yan sanda su biya diyyar Naira miliyan 25 kan matashin da suka kashe
Babbar Kotun Jihar Kano ta Biyar 5 da ke Sakatariyar Audu Bako ta umarci Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta biya Naira miliyan 25 a matsayin diyyar wani matashi mai suna Adamu Iliyasu wanda wani dan sanda ya bindige shi.Iyalan marigayin ne suka shigar da kara gaban kotun inda suke karar Mataimakin Sufeto Janar na […]
Babbar Kotun Jihar Kano ta Biyar 5 da ke Sakatariyar Audu Bako ta umarci Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta biya Naira miliyan 25 a matsayin diyyar wani matashi mai suna Adamu Iliyasu wanda wani dan sanda ya bindige shi.
Iyalan marigayin ne suka shigar da kara gaban kotun inda suke karar Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Shiyya ta daya da ke Kano da Kwamsihinan ’Yan sandan Jihar Kano bisa kisan dansu da wani dan sanda mai suna Saje Bello ya yi inda ya bindige shi a shekarar 2012.
Da yake yanke hukuncin Mai shari’a A.T. Badamasi ya ce kotunta yanke wannan hukunci ne bisa lura da yadda dan sandan ya kashe marigayin ba tare da laifin tsaye ko na zaune ba.