Kotu ta ci barawon wayar N15,000 tarar N200,000
Kotun ta yanke masa tarar N200,000.
A ranar Alhamis ’yan sanda suka gabatar da wani mutum mai shekara 36, a gaban kotun da ke Karu a Abuja, bisa zargin satar wayar salula wadda kudinta ya kai N15,000.
Wanda ake zargin da ke zaune a otel din Delta a yankin Nyanya a Abuja, na fuskantar aikata laifin sata.
Mai gabatar da kara, Olarewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Agusta, 2021.
Osho ya ce wanda ake kara ya gayyaci wata mata, Mary Monday, zuwa adireshin da aka ambata a sama sannan ya sace mata wayar salula samfurin Vivo, wacce darajarta ta kai N15,000.
Ya ce laifin ya saba wa sashe na 287 na Dokar Manyan Laifuka.
Alkalin kotun, Isa Anas, ya bayar da belin wanda ake tuhuma a kan kudi naira 200,000 da kuma wanda zai tsaya masa guda daya, sannan ya dage shari’ar har zuwa ranar 14 ga watan Oktoba don ci gaba da saurare.