Kotu ta ci dan sanda tarar N6m kan shiga gida babu izini
Kotu ta umarci dan sandan ya biya masu gidan da ya shiga ba izini N6m saboda ya tauye musu hakki
Kotu ta ci wani dan sana tarar Naira miliyan shida kan shiga gidan mutane ba tare da izini ba.
Alkalin Babbar Kotun da ke Osogbo, babban Birnin Jihar Osun, Mai Shari’a A. Oyebiyi, ya umarci dan sandan ya biya wadannan kudade ne ga Yusuf Adepoju da kuma Mudathir Kewdirorun, saboda take musu hakkinsu na ’yan kasa da ya yi.
- ’Yan bindiga sun fara harbin fasinjojin jirgin kasan da ke hannunsu
- Mahara sun kashe jami’an tsaro sun sace mutane a Kaduna
Masu karar dai sun bayyana wa kotun cewa a ranar 16 ga watan Yunin 2022 da misalin karfe 3:00 na dare ne dan sanda ba tare da wata gayyata ko kwakkwaran dalili ba ya afka musu gida.
Da yake yanke hukunci, alkalin ya ce laifin ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, da ya ba su ’yancin kare sirrinsu na cikin gida da iyalansu.