Kotu ta ci Fani-Kayode tarar N200,000

Kotun dai ta ci shi tarar ne saboda kin bayyana a gabanta.

Kotu ta ci Fani-Kayode tarar N200,000

Femi Fani-Kayode

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas a ranar Laraba ta umarci tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya biya tarar N200,000.

Kotun dai ta ci shi tarar ne saboda kin bayyana bayan an gurfanar da shi a gabanta, inda ya bayar da uzurin cewa hutawa yake yi.

A cewar kotun, dole wanda ake tuhuma ko dai ya dauki zabin warware belin wanda ake kara na biyu a shari’ar, ko kuma biyan tarar.

Muna tafe da karin bayani…

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya