Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano biliyan 30 saboda rusau a Filin Idi
Kotun ta ce za a yi amfani da kudaden ne domin biyan diyya ga masu shagunan
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Juma’a ta ci tarar Gwamnatin Jihar Naira biliyan 30 saboda rushe-rushen da ta yi a shagunan babban Filin Idi na birnin Kano.
Kotun ta ce za a yi amfani da kudaden ne domin biyan diyya ga wadanda aka yi wa rusau din ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da bin doka ba.
- HOTUNA: Gwamnan Kano Abba ya yi rusau a Filin Sukuwa
- Yadda muka tafka asara a rusau din Kano
- Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Filato
A watan Yuni ne dai Gwamnatin Jihar, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta jagoranci rushe shagunan, bisa zargin an yi su ba bisa ka’ida ba.
Sai dai jim kaɗan da yin hakan, gamayyar ’yan kasuwar suka maka gwamnatin a gaban kotun suna neman ta bi musu hakkinsu.
Sai dai da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, Alkalin kotun, Mai Shari’a Samuel Amobeda, ya ce matakin na gwamnatin Kano “jahilci ne da wuce gona da iri.”
Gwamnatin Kano dai ta yi zargin cewa wacce ta gabace ta ta Abdullahi Umar Ganduje ta sayar da filaye da kadarorin gwamnati, ciki har da filin masallacin na Idi.
To sai dai Ganduje ya musanta aikata ba daidai ba, inda ya ce ba shi ne Gwamnan Kano da ya fara sayar da filaye da kadarorin gwamnati ba.