Kotu ta ci ’yan majalisar Filato da ta kora tarar N128m
Kotu ta ci tarar ’yan majalisar dokokin jihar Filato da aka kwace kujerunsu a watan Nuwamban 2023, kudi Naira miliyan 128.
Kotun daukaka kara ta ci ’yan Majalisar Dokokin Jihar Filato wadanda aka kwace kujerunsu a watan Nuwamban 2023 tarar kudi Naira miliyan 128.
An ci ’yan majalisar su 16 tarar Naira miliyan 8 kowannensu ne bayan kotun ta yi watsi da karar da suka shigar na neman a sake neman ta sake duba hukuncin da ta yanke a baya na korar su.
Amma alkalan kotun da ke zama a Abuja karkashin jagorancin JOK Oyewole sun yi watsi da karar da cewa ba ta da tushe balle makama.
’Yan majalisar da aka kora, sun sake garzayawa kotun suna neman a dawo da su kan kujerunsu a majalisar dokokin jihar ne bayan da kotun koli ta tabbatar da zaben Ggwamna Caleb Muftwang.
- Ramadan: ’Yan kasuwa sun yi alkawarin daidaita farashin kayan abinci
- DAGA LARABA: Ruwan ‘Fiyowata’ Na Neman Ya Gagari Talaka
Amma bayan sauraron su, mai shari’a JOK Oyewole ya ki amincewa da kudirin saboda rashin cancanta, inda ya bayyana karar a matsayin bata lokacin shari’a.
Idan za a iya tunawa, kotun daukaka kara ta kori ’yan majalisar ne kasancewar jam’iyyarsu ba ta da shugabanci don haka ba za ta iya tsayar da ’yan takara a zabe ba.
A dalilin haka ne ta bayyana duk wadanda suka zo na biyu a zaben na 2023 a matsayin wadanda suka yi nasara.
Aminiya ta ruwaito cewa shugaban majalisar jihar, Gabriel Daweng, ya ki rantsar da ’yan jam’iyyar APC da na Labour 16 a matsayin ’yan majalisa a ranar 23 ga watan Janairu, inda ya ce ya samu umarnin kotu, inda ya bukaci su dakata har kotu ta yanke hukunci.