Kotu ta ci ’yan tumatir a kasuwar Sabon Gari tarar N50,000

Kotun ta umarci shugabannin kasuwar su gabatar da kansu a domin amsa tambayoyi.

Kotu ta ci ’yan tumatir a kasuwar Sabon Gari tarar N50,000

Kotu ta ci ’yan kasuwar tumatir da ke Kasuwar Sabon Gari a Jihar Kano tarar Naira dubu hamsin saboda karya dokar tsaftar muhalli.

A safiyar Asabar ce kotun tafi-da-gidanka kan kula da tsaftar muhalli ta Jihar Kano ta sanya wa ’yan kasuwar tarar bayan ta same su suna gudanar da harkokinsu, sabdanin Dokar Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Auwal Suleiman Yusuf, shi ne ya yanke hukuncin bayan samun ’yan kasuwar suna tsaka da harkokinsu, a lokacin zagayen tsaftar muhllin wanda ake gudanarwa a duk karshen wata.

Da yake yanke hukuncin, alkalin ya umarci shugabannin kasuwar ’yan tumatir din da su gabatar da kansu a Hukumar Muhalli ta Jihar Kano domin amsa tambayoyi.

Kotun, ta kuma ci tarar wasu kananan ’yan kasuwa da ta kama da laifin gudanar da kasuwanci a lokacin da dokar tsaftar muhallin ta karshen wata ta haramta.

Dokar Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano ta haramta bude kasuwanni da zirga-zirgar ababen hawa a duk ranar Asabar ta kowane karshen wata domin gudanar da ayyukan shara da tsaftar muhalli, sai an kammala ake fara hada-hadar kasuwanci da zirga-zirgar ababen hawa.

A lokacin zagayen tsaftar muhallin, Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dokta Kabir Ibrahim Getso ya ce, gwamnatin jihar ba za ta lamunci karya dokar ba, ko duk wani abu da zai cutar da al’ummar Jihar Kano.