Kotu ta ci ‘yan sanda tarar miliyan 15 saboda ‘yan Shi’a

Wata Kotun Tarayya da ke zamnata a Abuja ta umarci rundunar ‘yan sanda Najeriya ta saki gawar wasu ‘yan shi’a uku da jami’an rundunar suka kashe, kuma ta biya su tarar Naira miliyan 15. Kotun ta umarci a mika gawarwakin na ‘yan kungiyar IMN mabiya Shaikh Ibrahim El-Zakzaki ga iyalansu domin su yi masu sutura […]

Kotu ta ci ‘yan sanda tarar miliyan 15 saboda ‘yan Shi’a

Wata Kotun Tarayya da ke zamnata a Abuja ta umarci rundunar ‘yan sanda Najeriya ta saki gawar wasu ‘yan shi’a uku da jami’an rundunar suka kashe, kuma ta biya su tarar Naira miliyan 15.

Kotun ta umarci a mika gawarwakin na ‘yan kungiyar IMN mabiya Shaikh Ibrahim El-Zakzaki ga iyalansu domin su yi masu sutura tare da biyan su diyyar naira miliyan biyar kowannensu.

Sai dai alkalin kotun Mai Sharia Taiwo Taiwo ya yi watsi da bukatar da iyalan ‘yan shi’ar na neman rundunar ‘yan sandan ta nemi afuwarsu ta hanyar bugawa a jaridu ba.

‘Yan uwan mamatan da suka hada da Ibrahim Abdullahi da Ahmad Musa da kuma Yusuf Faska da Sa’id Haruna sun shigar da kara ne suna neman a ba su gawar mamatan da ake tuhumar jami’an rundunar da kashewa.

Mamatan wadanda suka hadar da Suleiman Shehu,  Mahdi Musa, Bilyaminu Abubakar Faskada Askari Hassan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin zanga-zangar lumana da suka yi a Abuja domin neman a saki jagoransu, Shaikh El-Zakzaki.

A lokaci ne ‘yan sanda  suka bude musu wauta suka kuma kai gawarwakinsu dakin ajiyar gawa na Babban Asibin Kasa da ke Abuja a ranar 22 ga watan Yulin 2019.

Masu shigar da karar sun bukaci kotun ta fayyace kisan da aka yi musu a matsayin haramtacce tare da tauye hakkinsu wanda sashi na 33(1)  da na 35 na kundin tsarin mulkin kasa suka ba su.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50