ICPC ta sake tsare El-Rufai
Kotu ta dage sauraron bukatar belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar Laraba
Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kasa (ICPC) ta sake kama tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sa’o’i kadan bayan addu’ar kwana uku da rasuwar mahaifiyarsa.
ICPC ta sake cika hannu da shi ne bayan babbar kotun da ke zamanta a Kaduna ta dage sauraron bukatar belinsa zuwa ranar Laraba.
Hakan na zuwa ne bayan an gurfanar da shi kan zargin aikata almundaha a zamanin mulkinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Tun da farko El-Rufai ya yi azumin watan Ramadan da Kamara Sallah a tsare a hannun hukumar, bayan ya gabatar da kansa a ofishinta domin amsa tambayoyi, kwanaki kadan bayan dawowarsa Najeriya daga kasar Masar.
Hukumar ta gurfanar da shi tare da ci gaba da tsare shi, kafin bayan sama da wata guda ta sake shi, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma, wadda Allah Ya yi wa rasuwa ranar Juma’a a kasar Masar, kafin a yi jana’izarta ranar Lahadi a Abuja.
ICPC ta sako shi ne bayan da farko kotu ta sanya Litinin din nan a matsayin ranar sauraron bukatar belin tsohon gwamnan.
Shaidu sun bayyana cewa bayan zaman kotun, jami’an Hukumar sun hana El-Rufai komawa gida, inda suka yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu.