Kotu ta dage shari’ar neman tube rawanin Sarkin Zazzau

Tsohon Wazirin Zazzau na kalubalantar rawanin Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Kotu ta dage shari’ar neman tube rawanin Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli

Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, ta dage shari’ar da tsohon dan majalisar nadin sarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad ya bukaci a tube rawanin Nuhu Bamalli daga sarautarsa ta Sarki.

Muhammad wanda shi ne tsohon Wazirin Zazzau kuma yana daya daga cikin wadanda suka nada Sarki Bamalli, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu mutane 13 a kotun, yana neman a tube rawanin Sarkin Zazzau na 19.

Daga cikin ragowar mutum 13 da ake kara har da Sarki Ahmed Nuhu Bamalli da marigayi Limamin Kona, Malam Sani Aliyu wanda ya riga mu gidan gaskiya a watan Yullin 2021.

Bamalli wanda tsohon Jakadan Najeriya ne a kasar Thailand, an nada shi Sarkin Zazzau na 19 a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020.

Nadin sarautar wanda Gwamna Nasiru El-Rufai ya yi na zuwa ne bayan Majalisar nadin sarki ta bayyana amincewarta.

Sai dai wanda akw kara sun yi watsi da bukatar a zaman kotun wanda Mai Shari’a Isah Aliyu ya jagoranta, suna masu cewar mai karar ba shi da hurumin gabatar da wannan bukata ta kalubalantar rawanin Sarki Bamalli.

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, lauyan Masarautar Zazzau, Abdul Ibrahim (SAN), ya ce suna kalubalantar karar ce la’akari da cewa mai ita ba ya cikin ko daya daga cikin wadanda gidajen da za su iya gadon sarautar ta Zazzau.

A nasa bangaren, lauyan mai jara, B.M Bello Esq., ya ce Sarki Bamalli bai cancanci sarautar Zazzau ba domin kuwa ba a kiyaye duk wasu tsare-tsare na al’ada ba gabanin nada masa rawanin.