Kotu ta dakatar da KANSIEC daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Kano
APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun kan zargin KANSIEC da saɓa wa ka’idodin shirya zaɓen
Wata Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da Hukumar Zaɓen Kano (KANSIEC) daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe.
Kotun mai zamanta a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S. A Amobeda ta bai wa Hukumar KANSIEC umarnin dakatar da duk wasu shirye-shirye na gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ta shirya gudanarwa a watan gobe.
- KANSIEC ta rage kuɗin takarar zaɓen ƙananan hukumomin Kano
- Tinubu zai yi wa majalisar ministocinsa sauye-sauye
Tun da farko Honorabil Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC suka shigar da ƙarar a gaban kotun suna neman ta dakatar da zaɓen har sai ta saurari gundarin shari’ar kan ƙorafin da suka gabatar.
A ƙunshin ƙarar da suka shigar, sun zargi hukumar ta KANSIEC da saɓa wa ƙa’idojin shirya zaɓe da kuma sanya kuɗin sayen fom ɗin shiga zaɓe, wanda suka ce ya wuce kima.
Aminiya ta ruwaito cewa, bayan sauraron ƙorafin, kotun ta sanya 4 ga watan Oktoba na bana a matsayin ranar da za ta fara sauraron shari’ar.
Idan za a iya tunawa, KANSIEC ta bayyana ƙudirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Kano a ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa.